Sabo Bakin Zuwo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Sake dubawa tun a 00:49, 30 ga Yuli, 2021 daga Mr. Sufie (hira | gudummuwa) (Sabon shafi: Shi ne gwamnan Kano mafi gajartar zango, ya zauna a wannan kujera na tsawon watanni biyu kawai. Shi mutumin unguwar Bakin Zuwo ne, wanda daga sunan unguwar ne ma ya samu Laƙabinsa na ‘Sabo Bakin Zuwo’. Wannan unguwa tana nan a cikin ƙwaryar birnin Kano . An haife shi a wannan unguwa ta Bakin Zuwo a ranar 31 ga watan Disamba na shekarar 1934. Karatu Duk da cewa bai yi nasarar fara karatun zamani tun yana ƙarami ba, ya fara ne da karatun Ƙur’ani a nan unguwar tasu ta Ba...)
(bamban) ←Canji na baya | Zubi na yanzu (bamban) | Canji na gaba → (bamban)

Shi ne gwamnan Kano mafi gajartar zango, ya zauna a wannan kujera na tsawon watanni biyu kawai. Shi mutumin unguwar Bakin Zuwo ne, wanda daga sunan unguwar ne ma ya samu Laƙabinsa na ‘Sabo Bakin Zuwo’. Wannan unguwa tana nan a cikin ƙwaryar birnin Kano . An haife shi a wannan unguwa ta Bakin Zuwo a ranar 31 ga watan Disamba na shekarar 1934. Karatu Duk da cewa bai yi nasarar fara karatun zamani tun yana ƙarami ba, ya fara ne da karatun Ƙur’ani a nan unguwar tasu ta Bakin Zuwo. Ya fara karatunsa na Zamani a makarantar Shahuci, inda ya halarci darrusan yamma (Karatun manya na yaƙi da jahilci). Daga baya ya shiga makarantar ‘Ibo (Igbo) Union School’ da ke Sabon Garin Kano. Sannan kuma ya zarce zuwa makarantar mulki ta zariya (Zaria administration Institute). Muƙaman da ya Riƙe Ya zama shugaban ƙungiyar ‘yankasuwa (United Labour Congress) reshen jahar Kano . Sannan ya zama mataimakin shugaba, na ƙasa, na wannan ƙungiyar. Ya yi aiki tare da kwamatin tantance masu karɓar bashi na jahar Kano (State’s Rent Assesment Committee). Sannan ya zama shugaban Hukumar Ƙayyade Farashi (Chairman Price Control Board). Sannan ya zama shugaban hukumar tsaftace kamfanoni (Chairman Indutrial Council Safety). Haka nan kuma ya taɓa zama shugaban Ƙungiyar ‘Yan’Dambe ta jahar Kano (State’s Ameteur Boɗing Association). Zamowarsa Gwamnan Kano Alhaji Sabo bakin Zuwo ya zama gwamnan jahar Kano ƙarƙashin tutar jama’iyyar PRP, bayan lashe zaɓen da aka gudanar a watan Agusta na shekarar 1983. Gudunmawarsa Duk da wannan ƙarancin lokaci da ya yi a kan kujerar gwamna, bai rasa abin ambato da ya bari ba, ya samu nasarar mayar da sinimar falas (Palace Cinema) da ke Unguwarsu ta Bakin Zuwo zuwa asibitin haihuwa (meternity home). Ana kiran wannan asibiti da sunansa.

< https://www.rumbunilimi.com.ng/KanoGwamnaBakinZuwo.html#gsc.tab=0\…